Boko haram: A kama Shekau cikin kwana 40 a mace ko a raye - umurnin babban hofsan sojin na ƙasa - CAMPUS94

Breaking

Entertainment, campus lifestyle, music

Post Top Ad

Post Top Ad

Saturday, 22 July 2017

Boko haram: A kama Shekau cikin kwana 40 a mace ko a raye - umurnin babban hofsan sojin na ƙasa

a kama shekau a mace ko a raye

Buratai ya ba kwamandan rundunonin dake yaki da ƙungiyar boko haram a arewa maso gabas umurni na su kama shugaban ‘yan ta’addan

Babban hafsan sojoji na ƙasa janar Yusuf Tukur Buratai ya umurci kwamandan rundunar sojoji na operation lafiya dole na garin maiduguri manjo janar Ibrahim Attahiru da ya kama shugaban ƙungiyar yan ta’adda cikin kwana 40.

A wata bayani da kakakin sojoji na ƙasa birgediya janar Sani Usman ya fitar a daren ranar juma’a, an umurci Attahiru da ya amfani da duk makamai dake tare da rundunar shi wajen kama jagoran ƙungiyar a duk inda yake boyewa.

Usman ya kara da cewa ana neman taimakon sauran ‘yan kasar wajen bada labari da zai taimaka wajen tabbatar da hakan ya faru.

SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here