Limaman da malamai zasu isar da sakon zaman lafiya ga mabiyan su yayin da ake zaben 2015 bayan horon wanda aka dakatar
Hukumar yaƙi da zurmiya ta ICPC ta ruwaito cewa jimillar N664M suka karkata akalar daga manufar su a hannun tsohon kwamishnan kudi na jihar Kebbi Alhaji Muhammed Tunga.
A rahton da jaridar Punch ta fitar, hukumar tana zargin Tunga tare da tsohon sakataren gwamnatin jihar Kebbi Alhaji Garba Kamba da sauya fasalin kudi da aka ware domin horon limamai da malaman jihar.
A wata takarda da kakakin hukumar Mrs Rasheedat Okoduwa ta karanto, N315M cikin kudin an ware su ne domin horar da limaman da malaman.
Limaman da malamai zasu isar da sakon zaman lafiya ga mabiyan su yayin da ake zaben 2015 bayan horon wanda aka dakatar.
Hukumar ta kara da cewa sauran N349M da ta rage an ware su ne domin siyan na’urorin samad da wutar lantarki wanda za’a sa a ko wani rumfar zabe kafin a gabatar da zaben 2015.
Bayan bincike da ma’aikatan hukumar suka yi aka gano hakan.
An gurfanar da Tunga da Kamba gaban mai shari’a Umar Abubakar na babban kotun jihar dake Birnin kebbi bisa ga zargin sauya akalar N664M.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment