![ASUU ta dakatar da yajin aiki](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7336761/8135291319-chorizontal-w1600/asuu-strike-2016-update.jpg)
Ƙungiyar ta umurci malamai da su koma bakin aiki daga ranar talata
Ƙungiyar malaman jami’o’i na Nigeria ta janye yajin aiki da ta shiga wadda ya kwashi sama da wata daya.
Shugaban ƙungiyar na kasa farfesa Biodun Ogunyemi ya sanar da haka bayan tattaunawar da suka da masu ruwa da tsaki na ma’aikatan ilimi da kwadago ranar litinin a garin Abuja.
Shugaban yace ƙungiyar ta amince da ta dakatar da yajin aikin don sun amince cewa gwamnatin zata biya bukatun su cikin watan Octoba bisa yarjejeniyar da suka sa hannu.
Ƙungiyar ta umurci malaman jami’o’i na ƙasa da su koma aiki daga ranar talata 19 ga watan Satumba.
Ogunyemi yayi kira ga gwamnati da kada ta sabawa yerjejeniyar da suka yi domin sun dakatar da yajin aikin don ganin cewa akwai aminci tsakanin ƙungiyar da gwamnati.
Shima ministan kwadago Chris Ngige yace ƙungiyar ta amince da ta dakatar da yajin aiki bayan jerin tattaunawa suka yi dasu kuma hakika malaman jami’o’i zasu koma aiki ranar talata bayan taron ƙungiyar a ko wani jami’a.
Ministan yace ƙungiyar da gwamnati sun amince da juna kuma sun fahimci juna.
A karshe ministan ya yaba wa ƙungiyar da ya yan ta inda yace duk wanda ke neman yadda zai gyara wajen aikin shi domin kowa ya amfana hakika ɗan kishin kasa ne.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment