![gwamanatin tarayya ta kaddamar da ranar litiniin a matasayin ranar hutu](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7388056/9085292285-chorizontal-w1600/Independence-day-Nigeria.jpg)
Dambazau yayi kira ga 'yan Nijeriya da su cigaba da bunkasa zaman lafiya da hadin kai a ƙasa
Gwamnatin tarayya ta bada ranar litinin 2 ga watan Octoba a matsayin ranar hutu.
An bada wannan hutun don murnar bikin cika shekaru 57 da samun yanci.
Bisa rahoton jaridar Vanguard, ministan harkokin cikin gida Lt.Gen Abdurahman Dambazau yayi wannan sanarwar.
A wata takada da sakatere na dindin na ma’katar Abubakar Magaji ya sa hannu, ministan yana ma 'yan Nijeriya barka na cika shekara 57 da samun yanci.
Dambazau yayi kira ga yan Nijeriya da su cigaba da bunkasa zaman lafiya da hadin kai a ƙasa.
Nijeriya ta samun yanci cikin 1 na watan Octoba 1960 bayan ta kwashi shekaru 59 karkashin mulkin Britaniya.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment