
Shugaban ƙwamitiin masu ba shugaban kasa shawarwari ya bayyana ainihin yawan kudin da ko wani sanata ke amsa duk wata a matsayin albashi
Shugaban ƙwamitin masu ba shugaban ƙasa shawarwari Farfesa Itse Sagay yayi suka game da yawan kudin da yan majalisa ke amsa ko wani wata.
Shugaban ya bayyana cewa ko wani sanata yana amsan miliyan N29.3 ko wani wata kuma biliyan N30.2 a duk shekara.
A rahoto da jaridar Nation ta fitar Sagay ya sanar cewa banda albashin da yan majalisa ke amsa ko wani akwai karin alawus na abubuwa da dama.
Yayi wannan bayani ne yayain da yake jawabi a wani taro da aka gabatar a Legas ranar talata 5 ga watan Satumba.
A jawabin shi Sagay ya zargi shugaban majalisa dattawa da son kai kuma baya taimakawa wajen ganin cewa an magance cin hanci da rashawa kamar yada shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yake yaki akai.
A karshe Sagay yace Æ™wamitin da yake shugabanta zata iya bakin kokarin ta wajen gurfanar da manyan ma’aikatan banki da ke taimakon masu satar kudin jama’a.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment