![Marigayi ya rasu yana da shekara 70 a duniya](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7253558/7775295228-chorizontal-w1600/KAsimu-Yero.jpg)
Gwamna El-rufai yace marigayi tauraro ne mai haskawa kuma ya sadukar da kanshi don ganin al'adar yan arewa ya kai ga ko ina
Fittacen tsohon dan wasan kwaikwayon hausa Alhaji Kasimu Yero ya rasu.
Kamar yanda labari yazo mana Alhaji Kasimu ya rasu yau ranar lahadi 3 ga watan satumba kuma anyi jana'izar shi a babban masallaci dake maiduguri road nan garin Kaduna bayan sallar la'asar.
Jaruman fina-finai hausa suna ta mika sakon ta'aziyya game da babban rashi da masa'antar tayi a shafukan su na kafafan tsada zumunta.
A sakon ta'aziya da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-rufai ya fitar ta hanyar kakakin sa Samuel Aruwan, gwamnan yace marigayi Alhaji kasimu tauraro ne mai haskawa kuma kwarewar sa ya taimaka wajen bunkasa al'adar yan arewa.
Marigayin ya rasu a garin Kaduna bayan doguwar jinya.
Kasimu yero ya fi yin fice a fagen sana'ar barkwanci kuma ya fice a shirye-shiyen da kafar watsa labarai na kasa (NTA) ke yi a shakara 1980 a cikin shirin "magana jari ce" da sauransu.
Kamar yanda ya wallafa a shafin sa na instagram, jarumin fina-finai hausa Ali Nuhu yana ma marigayi fatan Allah ya jikan shi.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment