Labari cikin hotuna: Ga abubuwan da suka gudana a hutun babban sallah - CAMPUS94

Breaking

Entertainment, campus lifestyle, music

Post Top Ad

Post Top Ad

Tuesday, 5 September 2017

Labari cikin hotuna: Ga abubuwan da suka gudana a hutun babban sallah

Abun nayi ne
Idan baku samu labari abubuwan da suka auku yayin da ake hutun bikin babban sallah toh ku kwantar da hankalin ku.
Ga abubuwan nan kasa;
1. Buhari yayi sallah a Daura
Shugaba Buhari yayi sallah a gidansa dake Daura tare da iyalinsa kuma ya samu ziyara daga mutane da dama ciki har da mai martaba sarkin Katsina da sarkin Daura da masu yi ma kasa hidima (NYSC).
Buhari da Sarkin Daura a filin idi

 
Sarkin Katsina ya kai ma shugaban ziyara
 
Buhari da iyalensa

suma masu yi ma kasa hidima sun ziyarci shugaban a Daura
 
 
2. Hawan Sallah
Ga yanda hawan sallah ya kasance a jihohin Katsina, Kano, Katsina, Gombe tare da garin Zaria.
A Gombe
sarkin Gombe

Hawa a Gombe

A Kano
sarkin Kano mai martaba Muhammad Sanusi

Hawan nasarawa

Sarkin Kano da tawagar shi
 
 
3. Yan Kwankwasiyya da Gandujiyya sun sari juna a jihar Kano yayin da ake hawan Daushe
anyi sare-sare tsakanin yan kwankwasiyya da Gandujiyya
 
Yayin da mutane da dama me murnar bikin sallah wasu magoyan bayan akidar kwansiyya da Gandujiyya sun nuna nasu inda su gwabza a fillin hawan daushe saboda siyasa.
sakamakon sare-saren
 
4. Allah yayi wa Shaharraren dan wasan Kwaikwayo rasuwa
Shaharren jarumin wasan kwaikwayo Alhaji Kasimu Yero ya rasu a Garin Kaduna ranar lahadi 3 ga watan satumba bayan daguwar jinyan rashin lafiya da yayi.
Ya mutu a garin Kaduna
 
Mutane da dama wadanda suka shahara a masana’antar fim da ma yan siyasa sun yi ta’aziyyar rasuwar rasuwar sa.
Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasiru El-rufai yace marigayi tauraro ne wanda ke haskawa don kuwa ya amfanin da kwarewarsa wajen bunkasa al’adar ‘yan arewa.
Gwamna El-rufai yayin da ya kai ziyarar ta'aziya ga iyalin marigayi
 
Shima jarumi Ali Nuhu yayi ma marigari fatan Allah ya gafarta mashi.
5. Fayose yaje sallar idi
Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya taya musulman jihar murna inda shima ya halarci sallar idi cikin manyan riguna.
Fayose a filln idi
 
6. Jaruma Halima Atete ta miko nata sakon barka da sallah daga kasa mai tsarki inda take aikin Hajj.
Halima Atete a aikin hajj na bana
 
fittaciyar yar wasan fim na hausa Halima Atete ta turo sakon barka da sallah zuwa ga masoyan ta daga kasar saudiyya inda take aikin hajj.
Jaruma mai tauraro ta tura sakon a shafin ta na Instagram.
daga shafin ta na instagram
 
 
7. Nigeria tayi wa Kamaru kaca-kaca a wasan kwallo
Tawagar super eagles
 
Tawagar yan wasan kwallon ƙasar Nigeria ta duki kasar Kamaru 4-0 a wasan Wasan Share Fage Na Gasar Cin Kofin Duniya Na 2018 ranar 1 ga watan satumba a garin Uyo.
Nigeria ta dauki Kamaru 4-0
 
A wasan su na biyu a garin Younde na Kamaru Nigeria da Kamaru sun tashi 1-1.
8. Tsagerun niger delta sun janye wa’adin da suka ba hausawa da yarbawa
Tsagerun sun mayar da bakan su na cewa yan arewa da yarbawa dake yankin su gaggauta su bar yankin.
Tsagerun sun janye wa'adin da suka bada
 
9. Sojoji masu yarkar Boko haram sunyi sallah a fagen daga
sojoji yayin da suke sallar idi
 
Suma sojojin dake yaki da yan boko haram sunyi sallah a fagen yaki har ma sun taka leda
Sojoji sun taka leda yayin da ake bikin sallah
 
10. Buhari ya watsa ma Ganduje kasa a ido
Ganduje bai ji da dadi ba
 
A bisa bayanin jaridar Daily Nigeria a ranar asabar da ta gabata ne shugaba Buhari ya ki ganawa da gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje bayan tattakin da gwamnan yayi takanas ta-kano zuwa Daura don ganawa da shugaban inda yake hutun bikin sallah.
Jaridar ta kara da cewa, wannan ya sa Gwamnan cike da takaicin da aka yi masa ya yanke shawarar kai ziyara ga 'yar Buhari, sannan kuma ya tsaya kallon hawan Daushe a nan Daura.
11. Bala Muhammaed ya ziyarci Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan
Tsohon minista ya ziyarci Jonathan
 
A ranar lahadi 3 ga watan satumba tsohon ministan birnin tarayya Sanata Bala Muhammed da tsohon ministan ayyuka na musamman Tanimu Turaki suka ziyarci tsohon shugaban ƙasa Jonathan a gidansa.
tsohon ministocin sun ziyarce shi a gidansa dake Abuja

wannan shine jerin labarai da Pulse hausa ta hada yayin da ake hukun bikin sallah.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here