![Shugaba Buhari ya iso London cikin lamin lafiya](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7361556/1715291926-chorizontal-w1600/President-Muhammadu-Buhari-at-the-72nd-session-of-the-United-Nations-General-Assembly-UNGA-in-New-York-on-Tuesday-September-19-2017.jpg)
Adesina yace Buhari ya iso London bayan ya halarci taron koli na majalisar dinkin duniya a New york
Shugaba Muhammadu Buhari ya iso birnin London bayan ya halarci taron koli na majalisar dinkin duniya da aka yi a New york ranar alhamis 21 ga watan Satumba.
Kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya bayyanar da isowar shi London.
Adesina yace Buhari ya iso London bayan ya halarci taron koli na majalisar dinkin duniya a New york cikin lamin lafiya.
“Tafiyar shugaban kasa na sati daya kuma tun ranar lahadi yayi tafiyar kuma ranar lahadi ko litinin zai dawo. Duk da cewa ya tafi London shugaban ba zai wuce yadda ya kayyade” yace.
Duk da cewa bai sanar da dalilin da yasa shugaban ya tafi London Adeshina ya bayyana ma gidan talabijin na Channels cewa shugaban ba zai wuce yadda ya kayyade ba.
Yayin da yake kasar Amurka wajen taron koli na majalisar dinkin duniya shugaba Buhari ya jawabi akan abubuwa dake faruwa a Nijeriya da ma duniyar baki daya. Kafin ya bar Amurka yaci abincn rana tare da shugaban kasar Donald Trump.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment