Bisa ga takardan wanan hanin ya fito ne domin matafiya da masu safaran kaya su samu sukuni wajen tafiyar da zirga-zirgan su a duk fadin ƙasa
Babban sufeton 'yan sanda na kasa Ibrahim Idris ya bada umarni na gaggawa ga jami’an hukumar da su daina tsaran hanyoyi a duk fadin kasar.
Wannan ya fito bayan wata takarda da kakakin hukumar Jimoh Moshood ya fitar ranar litinin 25 ga watan Satumba.
Bisa ga takardan wanan hanin ya fito ne domin matafiya da masu safaran kaya su samu sukuni wajen tafiyar da zirga-zirgan su a duk fadin ƙasa.
Cikin takardan babban jami’in yan sanda ya umarci jami’in hukumar dake safara a manyan tituna da hanyoyi da su sanya rigunan hukumar mai dauke da suna da lamba domin jama’a su gani.
Domin ganin cewa umarnin ya tafi kamar yadda ake so, hukumar ta kafa wata sabon runduna (special X-squad) wanda zata kama tare da yin bincike ko ta hukunta duk wani jami’in da ya aikata saɓanin wannan umarnin.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment