![SHugaba Buhari ya karrama shugabannin majalisar dokoki a fadar sa](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7518081/5805299328-chorizontal-w1600/Buhari.jpg)
Jagoran Buhari ya tabbatar da haka tare da saka hotunan taron su a shafin sa na twitter
Shuagaban ƙasa Muhammad Buhari a ranar alhamis 26 ga watan octoba ya karrama shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara wajen cin abinci ta musamman a faɗar sa.
Wannan yayi akasi da labari da kafofin yada labarai suka fitar na cewa shugabannin majalisar tare da mukarabban su basu samu damar shiga fadar shugaban ƙasa wanda yasa suka bar faɗar cikin ƙunci.
Jagoran shugaban a fannin kafafen sadarwa na yanar gizo Bashir Ahmad ya sanar da faruwar haka a shafin sa na twitter tare da hotu.
Shima mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo yana cikin wadanda suka halarci baje kolin cin abinci da shugaban.
Rahotanni sun nuna cewa jami'an tsaro na fadar shugaban ƙasa sun tsayar da tawagar shugabannin majalisar dokokin domin bincika motocin su kafin su shiga faɗar. Yan majalisar suna ganin yin haka bai kamata ba wanda daga bisani jami'an tsaron suka kulle kofofin faɗar shugaban har sai sun shirya amincewa da tsarin da aka umurce su da yi.
Yanzu dai sun daidaita tsakanin junansu.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment