![tawagar Nijeriya a gasar Common wealth na 2014](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7402433/3875298344-chorizontal-w1600/Team-Nigeria-Glasgow-2014.jpg)
Yayin da Nijeriya ke bikin murnar cika shekaru 57 da samun yancin. Akwai wasu shaguben ayyuka da suke faruwa cikin duhu
A ranar 1 ga Oktoba, 1960, yayin da Najeriya ta sami matsayi na 'yanci mai zaman kanta daga Ƙasar Ingila, Firaministan kasar Abubakar Tafawa Balewa ya ce sabuwar kasar zata kasance a kan hanyar zuwa ga nasara.
Ya ci gaba da nuna alfaharin sa ga abin da iyayen farko suka samu kafawa
"Yau Ranar yancin. Ranar Oktoban 1960 rana ce wanda tub shekaru biyu bayan yan Nijeriya ke neman isowar ta. Hakika wannan muhimmiyar ranar ta iso kuma yanzu Nijeriya ta kasance kasa mai yanci kai.” Balewa ya bayyana a babban filin da aka lika ma sunan shi dake jihar Legas
Ya kara da cewa; "Yanzu mun sami matsayinmu na gaskiya, kuma na tabbata cewa tarihi zai nuna cewa mun gina kasar mu a inda ya kamata. Nijeriya ta zauna a kan tushe mai tauri”.
Balewa ya karbi kaya na sabuwar kasa daga Gwamna Janar na Birtaniya, Sir James Robertson.
A tsakani filin da Balewa yayi jawabi akwai masu rawan gargajiya, kungiyoyin dalibai da masu rawan bada kama inda suka fallasa yin waka da rawa na murna.
A Saman filin Tafawa Balewa Square (TBS) dake jihar Legas inda Firayim Minista ya gabatar da jawabinsa, wasikun wuta ta haskaka samaniya da kuma waƙoƙin 'Ranar' Yanci na ta yaduwa a Nijeriya tun daga Legas zuwa Sokoto
Mu waiwaya baya
“Ina iya tunawa a baya tare da yin godeya ga Ubangiji yadda muka yi tsayuwa domin yin addu’o’i wanda babban faston cocin Anglican na jihar Legas tare da babban faston cocin katolika da babban limamin masallacin legas suka jagoranta” yadda tsohon gwamnan jihar filato Solomon Lar ya bayyana ma jaridar Vanguard.
“Duk sunyi ma kasar addu’a kuma a dai-dai karfe 12 na dare aka rage yawan hasken wuta kana aka mayar yadda take da sabon launin kore da fari wanda ta sauya tsohon tutar turawa.
“Duk munyi wakar taken kasa da kyakywan zato tare da halin kishin kasar mu, Nijeriya. A safiyar washe gari ne sarauniyar Ingila wanda ta wakilci daga gimbiyar Kent Alexandria ta bada kundin tsari cikin ladabi ga firam minista Abubakar Tafawa Balewa.”
Juyin mulki
Bayan juyin mulkin sojoji da aka yi a shekaru baya tsakanin 1960 zuwa 1990, Nijeriya ta amince komawa ga mulkin dimokradiya.
A cikin 1999, Olusegun Obasanjo wanda yayi mulkin kasa a zamanin mulkin soja bayan juyin mulki da aka yi ma Janar Murtala Muhammed ya kasance sabon shugaban kasa wanda aka zaba a mulkin dimokradiyya karkashin jam’iyar PDP. wannan ya gfaru bayan kai-kawon da kasar ta fuskanta a shekaru baya.
A cikin 2015 Obasanjo yace Nijeriya tana samun isasshen cigaba duk da kalubalen da take fuskanta.
Tsohon shugaban kasa ya kara da cewa kasar ta koyi darasi daga kuskuren da ya faru a baya kuma ta shirya samun nasara nan gaba.
Ya bayyana haka yayin da yake hira da yan jarida a garin Abeokuta a cikin 2015,
Cigaba da gwajin mulkin dimokradiyya
A cikin watan Maris na 2015, shugaba Muhammadu Buhari ya amshi tutar shugabancin kasa bayan jam’iyar adawa ta APC ta samu nasara a kan PDP a zaben wanda aka kasa, tare da tsare kuma aka raka har inda ma’aikatan hukumar zaben suka kirga.
Shugaban ya ci nasara kasancewar alkawullan da ya dauka yayin da yake kamfen neman zabe inda yace zai yi maganin cin hanci da rashawa, zai kawo karshen ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasa kuma zai bunkasa harkan kasuwanci na kasa.
Yayin da Nijeriya ke murnar shekara 57 da samun yanci shugaban yadukufa akan alkawullan da ya dauka shekara biyu bayan saura shekara biyu zaman shi na zama shugaban kasa a mulkin demokradiyya zai zo karshe.
Masu yunkurin a raba kasa
Nijeriya tana fama da masu yunkurin a raba kasa daga al’ummar yankin kudu maso yamma da yan kudu maso kudancin kasar. A kwanan baya sojoji sun gwabza da wasu daga cikin masu yunkurin kafa sabon kasa a jihar Abia.
Da haka shugaban yake kara jaddada cewa kasar baza ta rabu ba karkashin shugabancin shi kuma zai yi iya bakin kokarin shi wajen ganin cewa kasar ta samu cigaban da ya kamata.
Shugaban ya bayyana cewa kasar ta samu sabon yancin siyasa kasancewar shi shugaba. Yayi tsokacin cewa masu yunkurin raba kasa basu san alamarin da ya faru a cikin 1967 yayin da aka yi yankin kasa.
A karshe dai shugaban yayi masu shawara cewa indai zasu cigaba da yada manufar su toh lalle sai sun bi hanyar da ya kamata.
“Zamu cigaba da yarjejeniyar tsakanin gwamnati da al’ummar Niger Delta domin tabbatar da zaman lafiya. Muna kokarin magance masololi dake al’ummomin yankin ke sufkanta” shugaban ya dau alkawari.
Da shima shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki kara da cewa zaman lafiya shine babban kaddara da kasar take dashi.
Shima gwamnan jihar Osun Rauf Aregbesola yace “karfin mu yana cikin hadin kan mu. Kada mu bari wani abu ya gurbatar da hadin kan mu tare da kyakyawan zamantakewar mu "
Tutar mu abun alfaharin mu
Shuagabannin siyasa har yanzu suna da yakinin ganin kasar ta samu nasara duk da cewa suma suna cikin manyan kalubalen da tayi sanadiyar rashin zuwan kasar ga jerin manyan kasashe a duniya.
Har yanzu dai akwai masu kishin kasa a cikin titunan mu. Mutanae na daura tutar kasar a motocin su har da gidajen su a duk fadin kasar tun makonin baya kafin isowar ranar murnar ciak shekaru 57 da samun yanci na wannan shekara. Cikin ofishoshi har da gidajen cin abinci muna ganin yadda aka sanya tutar kasar a duk fadin kasa.
Masu motocin haya da yan babur suma sun tofa albarkacin su ga kasa inda suma sun daura tambarin kasar a sama gilashin motocin su har da saman kansu.
“kasar mu zata samu nasara. Ina mai tabbatar wa cewa zamu kai ga manufar mu” cewar wata Titilayo yayin da take murnar bikin yanci inda tayi ma fuskan ta fenti da launin kasar.
Shima wani ma’aji mai suna Henry yace yayi amanna da samun nasara a kasar.
Hakika akwai abun alfahari cikin tutar kasar inda tun makonin baya yan kasa ke nuna ma duniya muhimmanci shi a rayuwar su.
Shekaru 57 kenan da Tafawa Balewa yayi jawabi cikin lumana ga yan kasa yayin da kowa ke farin cikin samu nasarar zama kasa mai zaman kanta. Bayan haka kasar Britaniya ta saukar da da tutar su inda aka sauya da sabon tutar Nijeriya mai launin kore da fari.
Duk da cewa ta kwashi shekaru 57 bata cinma burin ta ba har yanzu dai akwai kamshin samun nasara nan ba da jimawa ba.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment