![Isowar Shugaba Buhari kasar Turkiya tare da uwargidan sa](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7481771/1045299274-chorizontal-w1600/22549508-1422123151219444-4861602356057420609-n.jpg)
Shugaban ya gana da mataimakin ministan harkokin ƙasashen waje Ahmed Yildiz a filin jirgin Esenboga dake nan Ankara
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya iso kasar Turkiya tare da uwargidan sa Aisha Buhari da sauran mukarraben sa.
Shugaban zai halarci taron majalisar D-8 a garin Istanbul inda zai kara haske akan yanda harkar kasuwanci ke bunkasa a ƙasar Nijeriya bugu sa kari zai jawo hankulan ƙasashen kan zuba jari da hada gwiwa domin tallafawa dukannin ƙasashen.
Shugaban ya gana da mataimakin ministan harkokin ƙasashen waje Ahmed Yildiz a filin jirgin Esenboga dake nan Ankara yayin da suka sauka jirgi.
Cikin tawagar shugaban da suka raka shi ƙasar akwai shugaban hukumar kwastam Kanal Hameed Ali da ministoci da wasu ma'aikatan fadar sa tare da yaran sa biyu Yusuf da Halima.
Ana ƙyautata zaton cewa shugaban hukumar kwastam na Nijeriya zai tattauna da gwamnatin ƙasar bayan taron game da shigowa da makamai da aka yi kwanan baya daga ƙasar daga bisani zasu tattauna akan yadda za'a kawo karshen yiwuwar hakan.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment