Garba Umar: Tsohon gwamna ya bayyana Dalilin daya sa ya canja sheka zuwa jam'iyar APC - CAMPUS94

Breaking

Entertainment, campus lifestyle, music

Post Top Ad

Post Top Ad

Friday, 17 November 2017

Garba Umar: Tsohon gwamna ya bayyana Dalilin daya sa ya canja sheka zuwa jam'iyar APC

Tsohon gwamnan jihar Taraba Garba Umar

Ya fadi haka a garin Jalingo yayin da ya gabatar da kansa tare da mabiyan sa babban ofishin jam'iyar na jihar Taraba

Tsohon mukaddashin gwamnan jihar Taraba Garba Aliyu ya bayyana dalilin da sa ya  canza sheka zuwa jam'iyar APC tare da mukarraben sa.

Ya fadi hakan a garin Jalingo babban birnin jihar yayin gabatar da kansa a babban ofishin jam'iyar APC tare da mabiyan sa.

"Na dade ina lura da yadda alamura ke tafiya a jam'iyar APC kana na lura cewa jam'iya ce mai kwatanta adalci ga mabiyan ta." yace.

Garba ya kara da cewa ya koma jam'iyar APC domin taimaka mata wajen samun nasara a zaben 2019 na jihar.

Yayi kira ga jam'ar jihar da su tsaya tsayin daka da jam'iyar APC wajen kawar da jam'iyar adawa ta PDP daga gidan gwamnatin jihar a zaben 2019.

Yayin tarban shi a farfajiyar su, shugaban jam'iyar APC na jihar Alhaji Sani Chul ya jinjina wa tsohon mukaddashin gwamna bisa ga matakin da ya dauka na dawowa jam'iyar.

Yace zaman Garba a jam'iyar zai taimaki jam'iyar wajen samun nasara a zaben 2019.

SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here