Majiya sunce sun gana ne cikin sirri domin tattaunawa akan kuran da batun tsohon shugaban kwamintin gyaran fuska ta fansho Abdurasheed Maina ya tada
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da ministan ayukan cikin gida Abdurahman Dambazau sunyi ganawan sirri ranar alhamis 2 ga watan Nuwamba.
Majiya sunce sun gana ne cikin sirri domin tattaunawa akan kuran da batun tsohon shugaban kwamintin gyaran fuska ta fansho Abdurasheed Maina ya tada.
Ana zargin Dambazau da shugaban hukumar ma'aikata Winifred Oyo-ita da sa hannu wajen komawar Maina aiki.
A baya dai Ministan ya musanta wannan zargin cikin wata takarda da kakakin sa Ehisienmen Osaigbovo ya fitar bayan sa hannun shi.
A cikin takardar ministan yace Maina ya koma aiki ne ta hanyar hukumar ma'aikatan kasa domin ma'aikatare shi bata da damar yin haka.
Batun Abdurasheed Maina ya janyo tsegumi a kasar har ma jama'a da dama suna korafi akan gwagwarmayan da shugaba Buhari keyi kan kawar da cin hanci da rashawa a kasar.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment