![Gwaman jihar Imo Rochas Okorocha](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7632565/4305298391-chorizontal-w1600/Imo-State-Governor-Rochas-Okorocha.jpg)
Gwamnan yayi kira ga jama'a da su goyi bayan zarcewar shugaban a zaben 2019
Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha yace shugaba Muhammadu Buhari shine mafi cancanta a takarar shugaban ƙasa na zaben 2019.
Gwamnan yayi kira ga jama'a da su goyi bayan zarcewar shugaban a zaben 2019.
Okorocha ya fadi haka a garin Oweri ranar talata 21 ga watan nuwamba yayin da ya karbi bakonci shugabannin ƙungiyar "Democratic youth congress for buhari 2019" yayin da suka ziyarce shi a fadar gwamnatin jihar Imo.
Duk da cewa shugaba Buhari bai bayyana kuddirin fitowa takara a zaben 2019, akwai alamu mai nuna cewa
"Shugaba Buhari shine mafi dacewa a kasar mu a halin yanzu kuma ina ganin babu wanda ya fi shi cancanta.
"Na Amince da shugabancin shi kuma na bayyana tun a baya cewa idan har shugaba Buhari ya fito takarar shugaban kasa ba zan kuskura in fito ba.
"Gashi Allah yayi shine shugaban kasar Nijeriya kana da yawa cikin mu mun shaida cewa Buhari shine mafi cancanta wajen jagorancin kasar a wannan halin da kasar take ciki." Gwamnan yace.
Karanta: Dalilin da yasa gwamna ba zai iya fitowa takara a zaben 2019
Okorocha ya kara da cewa gwamnonin jihohin Nijeriya banda na jihohi biyu suke goyon bayan zarcewan shugaban a karagar mulkin ƙasar.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment