![Attiku Abubakar](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7681548/9876209235-chorizontal-w1600-q90/Atiku-Abubakar.jpg)
Yana mai cewa "na dawo gida" domin babban dalilin da ya sanya na bar jam'iyar PDP an warware ta
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyanar cewa ya koma jam'iyar adawa ta PDP.
Ya sanar da haka a kafar safar sada zumunta ta facebook kai tsaye ranar lahadi 3 ga watan Disamba.
Yana mai cewa "na dawo gida" domin babban dalilin da ya sanya na bar jam'iyar PDP an warware ta.
Shi dai Atiku Abubakar yayi murabus daga jam'iyar APC cikin makon da ya gabata inda yake yiwa jam'iyar zargin cewa bata cinma burin yan Nijeriya ba kana bata kwatanta hakikanin tsarin dimokradiya.
Karanta Tsokacin gwamna yayi game da ficewar Atiku daga jam'iyar APC >> Babu Mai farin jinin shugaba Buhari
Ficewar shi daga Jam'iyar APC bata razanar da wasu da dama ba domin ana ganin cewa zai sauya zuwa jam'iyar PDP domin kaddamar da kuddirin sa na zama shugaban kasar Nijeriya a 2019.
Hirar sa da Dele Momodu, mai wallafa mujallar Boss magazine a cikin hutun karshen mako, Atiku ya sanar cewa Shugaba Buhari bai da farin jini kamar yadda yake dashi a da kana ya kara da cewa zai kada shugaban a zaben 2019.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment