![Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7627531/9715295246-chorizontal-w1600/sheik-amuludun-fayose.jpg)
Wannan tsokacin nasa ya fito ne bayan da gwamnatin taraya ta nemi a ware $1B domin bunkasa harkar tsaro a kasa daga kudin asusun arzikin man fetur.
Gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya gardadi gweamnatin tarayya na mayar da hankalin kan mawuacin ahalin da al'ummar jihar suka shiga wanda ya kira da "yunwa Haram" ba Boko Haram.
Gwamnan ya kara bada shawara na ayi amfani da dala biliyan guda wanda aka ware domin yakar boko haram zuwa bangaren wanzar da matsaloli da kasar ke fama dasu.
Wannan tsokacin nasa ya fito ne bayan da gwamnatin taraya ta nemi a ware $1B domin bunkasa harkar tsaro a kasa daga kudin asusun arzikin man fetur.
Shi dai Fayose ya nemi a ware nashi kason na daga cikin kudin domin al'ummar jihar sa na fama da yunwa wanda ya wuce yakar Boko haram.
Gwamnan dai ya sanar cewa ya kai kara kotu domin yin haka hakkin sa ne a matsayin sa na jagoran jihar.
A bayanin sa bayan taron gwamnoni, gwamnan jihar Bayelsa Seriake Dickson ya goyi bayan yunkurin da gwamnatin tarayya ke neman yi na ware $1B domin inganta tsaro a kasa inda yake cewa hakan ma manufa ce kyakyawa.
Dickson yace yunkurin bata da halaka da harkar siyasa domin manufa ce wanda zata bunkasa harkokin tsaro a kasa don amfanin kowa da kowa.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment