Hukumar Kwastam: Adaddin kudin da hukumar kwastam ta samu tsakanin watan janairu zuwa watan nuwamba na bana - CAMPUS94

Breaking

Entertainment, campus lifestyle, music

Post Top Ad

Post Top Ad

Wednesday, 20 December 2017

Hukumar Kwastam: Adaddin kudin da hukumar kwastam ta samu tsakanin watan janairu zuwa watan nuwamba na bana

Hameed Ali

Attah yace dalilin da ya sanya darajar bana ta wuce na bara shine yawan kame-kame da suka yi na motocin alfarma.

Hukumar hana shigowar kayan fasa kwabri ta kasa ta kama adadin kaya 3,870 mai darajar biliyan N11.2 daga watan janairu zuwa Nuwamba na 2017.

Kakakin hukumar Mista Joseph Attah ya sanar ma manema labarai dake garin Abuja hakan ranar talata tare da bayyana cewa anyi hakan cikin dattako.

Attah yace dalilin da ya sanya darajar bana ta wuce na bara shine yawan kame-kame da suka yi na motocin alfarma.

Yace a cikin 2016 ne shugaban hukumar kanal Hameed Ali mai ritaya ya gabatar da wasu tsare tsare na canja fasalin hukumar wanda dalilin hakan ya sanya aka samu nasara a 2017.

  • Hukuma ta kama wata mahaifiyar yara 7 mai fataucin ganyen wee-wee

Kakakin ya nuna cewa kayan aemashi suka kama bana kuma hakan ya taimaka wajen bunkasa harkar kasuwanci a kasar kana ya taimaka wajen inganta rayuwan yan kasar ta bangaren tsaro.

Daga karshe Attah yace muhimmin abun da zai faru da kayayyakin da suka kama shine za'a baje su a matsayin kayan gwanjo bayan amincewar doka da gwamnatin tarayya.

SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here