Yusuf Buhari: Har yanzu Yusuf na jinya a Nijeriya, bai tafi kasar waje - CAMPUS94

Breaking

Entertainment, campus lifestyle, music

Post Top Ad

Post Top Ad

Thursday, 28 December 2017

Yusuf Buhari: Har yanzu Yusuf na jinya a Nijeriya, bai tafi kasar waje

Buhari's son, Yusuf, suffers head injury in bike accident

Kakakin shugabankasa yayi watsi da labari dake yaduwa cewa an tafi da Yusuf Buhari kasar waje domin jinya

Fadar shugaban kasa ta sanar cewa har yanzu dan shugaban kasa Yusuf Buhari yana nan asibiti cikin Nijeriya ba'a tafi dashi kasar waje.

Babban mai yi wa shugaban hidima a fannin watsa labarai Garba Shehu ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar ranar alhamis 28 ga watan Disamba.

 

A bisa ga rahoton da jaridar The Cable ta fitar, ana zargin cewa an tafi da Yusuf kasar Jamus domin jinyar raunin da ya samu sanadiyar hatsarin babur da ya samu safiyar ranar alhamis.

Shi dai kakakin wanda shine ya sanar da labarin hatsarin ga jama'a yace har yanzu Yusuf na nan a wata asibitin kudi inda yake jinya kana ya kara da cewa labarin dake yaduwa na cewa an tafi dashi kasar waje labari ne mara tushe.

Karanta>> Ya dace shugaba Buhari ya zarce da shugabanci - inji Garba Shehu

A safiyar ranar laraba 27 ga wata Shehu ya sanar cewa Yusuf Buhari ya ji rauni tare da karaya sanadiyar hatsarin babur da ya samu a yankin Gwarinpa nan babban birnin tarayya daren ranar 26 ga watan yau.

SHi dai kakakin ya sanar cewa anyi Yusuf tiyata kuma yana murmurewa.

Daga karshe kakakin ya sanar cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana mika godiya ga yan kasar bisa addu'o'i da suke yi game samun lafiyar dan shi.

posted by Campus94

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here