![Shugaba Buhari ya kori Babachir Lawal](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7532087/6155294521-chorizontal-w1600/babachir-lawal.jpg)
Jami'an hukumar sun kama Babachir Lawal jiya laraba 24 ga wata bisa ga laifufuka da ake zargin sa da aikatawa.
Hukumar dake yaki da masu yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta kama tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal.
Jami'an hukumar sun kama Babachir Lawal jiya laraba 24 ga wata bisa ga laifufuka da ake zargin sa da aikatawa.
A kwanan baya ne shugaba Muhammadu Buhari ya kori tsohon sakaren gwamnatin sa bisa ga rahoto da kwamitin da kaddamar suka bayanar mashi.
Kwamitin wanda mataimakin shugaban kasa ya jagoranta, an kafa ta ne domin gudunar da bincike kan zargin karkatar da kudaden da aka ware ma 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram komai ya daidaita.
*Wannan matashi yana shirin fitar da Shugaba Buhari daga fadar Aso Villa
Bisa ga bincike da kwamitin tayi an kama Babachir Lawal da laifi.
Hakazalika kwannan baya yan majalisar dattawa sun sameshi da laifi duk a kan wannan batun.
Kodai sukar da tsohon shugaban kasa yayi tayi tasiri?
Wannan sabon yunkurin ya fita kwana biyu bayan sukar da tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo yayi ma gwamnantin shugaba Buhari.
A cikin wasikar da ya fitar ma manema labarai tsohon shugaban ya zargi gwamnatin Buhari da yin tafiyar hawainiya wajen hukunta masu yi wa tattalin arzikin na kasa zagon kasa.
Kan wannan wasu yan Nijeriya da dama ke jingina wasika da yin tasiri wajen yunkura ma gwamnatin wajen yin aikin da ya kamata.
posted by Campus94
No comments:
Post a Comment