![Diyar marigayi Rabilu Musa Ibro zata shiga sahun sabbin amare](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7865640/8745299037-chorizontal-w1600/UNSET-.jpg)
Za'a daura su tare da angon ta Saleh Isa a garin Danlasan Warawa dake karamar hukumar Wudil nan jihar Kano
Jawahir diyar shahararren dan wassan kwaikwayo marigayi Rabilu Musa Ibro zata shiga cikin sahun sabbin amare kwanan nan.
Za'a daura aurenta da angon ta Saleh Isa ranar 20 ga watan Janairu.
*Hotunan bikin fitaccen mawaki da sabuwar amaryar shi
Babban jarumi kuma mai shirya fim din hausa Falalu Dorayi ya sanar da wannan a shafin shi na Instagram.
kamar yadda ya wallafa a shafin shi za'a daura auren ne a Danlasan warawa dake karamar hukumar Wudil nan jihar Kano ranar asabar 20 ga wata.
*Manyan jarumai sun halarci bikin taya murna zagayowar ranar haihuwar Jaruma
*Kalli hotunan jarumi tare da matar shi inda yake narkar da zuciyar ta da kalamun soyayya
Ana gayyatar kowa da kowa wajen wannan taron aure.
posted by Campus94
No comments:
Post a Comment