![Abubakar Shekau threatens to cause more havoc in North-East](https://static.pulse.ng/img/news/crop7923443/9725292054-chorizontal-w1600/f6257be379b6b3f01d054f961f6b6e8d1baef36c.jpg)
Jagoran kungiyar yan ta'addar Boko haram Abubakar shekau ya bayyanar a cikin faifan bidiyo wanda aka fitar ranar talata 6 ga watan febreru cewa rundunar sojojin kasa sunyi karya inda suke cewa sun samu nasarar fatattake su.
Gawurtaccen shugaban kungiyar ta'adanci dake yi ma kasa zagon kasa ta Boko Haram ya fitar da sabon faifan bidiyo inda ya mayar ma sojoji martani bisa sanarwar da tayi na cewa an kore su daga dajin sambisa.
A kwanan baya ne kwamandar rundunar operation lafiya dole manjo janar Rogers Nicholas ya sanar cewa sun samu nasarar korar yan kungiyar boko haram daga dajin sambisa.
Jagoran kungiyar Abubakar shekau ya bayyanar a cikin faifan bidiyo wanda aka fitar ranar talata 6 ga watan febreru cewa rundunar sojojin kasa sunyi karya inda suke cewa sun samu nasarar fatattake su.
A cewar shi, yanzu ma suka fara kuma duk wanda ke tunanin cewa an halaka su, ya sani cewa idan har ya sa kafar shi a dajin sambisa sunan shi zai koma gawa.
Bisa ga sakon shi, har yanzu suna kan bakan su na yakar Nijeriya da ma duk wanda ke goyon bayan karatun boko.
posted by Campus94
No comments:
Post a Comment