![Ali Nuhu da Adam Zango sun sasanta](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7954055/6855295284-chorizontal-w1600/kannywoodcelebrities-8-2-2018-10-59-4-6.jpg)
Wannan sasanci ya faru ne bayan kokarin da wasu masu ruwa da tsaki a masana'antar fim suka yi domin sasanta su
Shaharrarun yan wasan fim na masana'antar Kannywood Ali Nuhu da Adam Zango sun sasanta da juna.
Bisa wannan sabon al'amari an kawo karshen tsabanin da ya faru tsakanin jarumai wanda ya haifar da takaddama tsakani magoyan bayan su a kafar sada zumunta.
Wannan sasanci ya faru ne bayan kokarin da wasu masu ruwa da tsaki a masana'antar fim suka yi domin sasanta su.
A gudanar da zaman neman sasanci ne a ofishin shugaban hukumar tace fina- finai na jihar kano Alhaji Isma'il Na'abba Afakallahu.
Cikin jiga-jigan masana'antar da suka halarci wannan zaman sasanci sun hada da Falalu Dorayi da Nura husseini da sakataren kungiyar masu shirya fim Sani Sule Katsina.
Falalu Dorayi ya rubuta a shafin sa tare da wallafa hoton su tare bayan kammala zaman neman sasanci.
"Alhamdulillah.
Alhamdulillah.
Alhamdulillah.
An kammala Ganawa cikin alkairi. Ali Nuhu da Adam A Zango
Allah ya kara hada kawunanmu.
Allah ka tsare Film industry daga dukkan masifu. Ya bamu zama lfy.
Ku kuma Ismail Naabba_Afakallah da Sani Sule da Hussain Nura
Allah ya biya ku. Ameen." Ya rubuta.
Suma dai jarumai sun wallafa sakamakon zaman da suka yi da jiga-jigan a shafukan su.
Wannan uya nuna cewa komai ya warware tsakanin su kuma za'a cigaba daga inda aka tsaya wajen nishadantar da jama'a.
posted by Campus94
No comments:
Post a Comment