Abun al'ajabi: Mahaifiya ta haifi jaririya mai hannu 4 da kafa 3 a Kaduna - CAMPUS94

Breaking

Entertainment, campus lifestyle, music

Post Top Ad

Post Top Ad

Monday, 5 March 2018

Abun al'ajabi: Mahaifiya ta haifi jaririya mai hannu 4 da kafa 3 a Kaduna

Malama Hauwa'u tare da diyar ta

Mahaifiyar mai suna Malama hauwa'u Jamilu ta haifin yaran ne a ranar lahadi 25 ga watan febreru.

Wata mahaifiya a garin kaduna ta haifi tagwaye daya daga cikin su tana da hannu hudu da kafa uku.

Mahaifiyar mai suna Malama hauwa'u Jamilu ta haifin yaran ne a ranar lahadi 25 ga watan febreru 2018.

Kamar yadda jaridar Daily trust ta fitar da labari, ta rungumi kaddara bisa halittar da daya daga yaran nata.

Duk da aibin da jama'a ke mata tana mai cewa babu yadda za'ayi da kaddarar Allah kuma tana farin cikin samun yaran kamar yadda ko wace mahaifiya take kaunar yaran cikin ta.

"Hakika mutum zai so samun jariri cikin koshin lafiya ba tare da  wani nakasa ba. Amma tunda Allah cikin rahamarsa ya kaddara zan samu tagwaye cikin wannan hallitar, babu da zan iya yi. Don haka kuka ganni cikin walwala kuma ina matukar kaunar su.

Banda wannan nakasin da daya daga cikin tagwayen take dashi, komai nata yana nan kamar sauran jarirai.

Idan ba'a manta ba na dauke ta cikin ciki na na tsawon watanni tara. Ina son diya ta kuma ita ma halitar Allah ce kamar sauran mutane duk da nakasin da ta fito dashi" ta sanar ma manema labarai.

Malama Hauwa'u wanda wannan shine karo na hudu da take haihuwa ta bayyana cewa bata zuwa awo asibiti kuma a gida ta haifi duk yaran ta.

Sai dai wani kwararren likita a asibitin koyo na jami'ar Ahmadu Bello mai suna Dakta Umar Abdul'aziz yace za'a iya yi ma diyar aiki domin cire karin hannu da kafa da ta fito dashi kuma tana iya cigaba da rayuwar ta kamar yadda ya kamata.

posted by Campus94

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here