![Magoya bayan Sanata sun raka shi kotu inda bisa laifin bada labarin karya](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop8054836/3665299282-chorizontal-w1600/Dino-court-702x336.jpg)
Ana zargin dan majalisar dattawa da yin karya wajen bada labarin
Dan majalisar dattawa Dino Melaye ya ziyarci babban kotun tarayya dake garin Abuja tare da wasu abokan aikin sa da magoya bayan shi.
Sanata Shehu Sani da Ben Murray Bruce sun raka abokin aikin su zauren kotun a zaman da aka yi kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar a kan sa.
Magoya bayan Dino, suna dauke da kwalaye da fastoci masu dauke da hotunan sa, kuma an rubuta “Mu na bayan Dino Melaye” da manyan rubutu a jikin kowace babbar fasta.
Ana tuhumar Dino Melaye da laifi kan labarin karya da ya bada na cewa ana barazanar neman kashe shi.
A karar da ofishin ma'aikatar shari'a na tarayya ta shigar ranar 31 ga watan janairu 2018, ana zargin Dino Melaye da bada shaidar karya ga mataimakin gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello mai suna Edward Onoja David tare da bada labari karya mara inganci.
posted by Campus94
No comments:
Post a Comment