Za'a hukunta duk wanda ke da hannu wajen hadassa rikici a jihar musamman a kudancin jihar
Gwamnatin jihar Kaduna ta sha alwashin hukunta duk masu haddasa rikici a jihar musamman a kudancin jihar.
Gwamnan jihar Malam Nasir El-rufai ya bayyana hakan yayin da ya gana da manema labarai a Kaduna.
Wannan sanarwar ya fito sakamakon rikicin da ya barke a garin Kasuwar magani na jihar sati biyu baya wanda yayi sanadiyar kona gidaje da dama tare da hallaka mutane.
Rikicin ya samu asali ne bayan wata matashiya kirista ta sauya addinin zuwa musulunci bisa soyayya da take da wani musulmi.
Kan rikicin da ya tayar da kura a jihar, gwamnan jihar yana zargin wasu yan siyasa na yankin da hura wutar rikicin wanda ya yi sanadiyar asarar dukiyoyi da rayuka.
Tun ba yau ba jihar ke fama da rikice-rikice dake da nasaba da kabilanci ko addina kuma gwamnati ta sha daukan alkawarin kawo karshen yiuwar hakan.
posted by Campus94
No comments:
Post a Comment