Ali Nuhu: Dalilai 10 da yasa jarumi ya zama abun koyi a masana’antar Kannywood - CAMPUS94

Breaking

Entertainment, campus lifestyle, music

Post Top Ad

Post Top Ad

Wednesday, 20 September 2017

Ali Nuhu: Dalilai 10 da yasa jarumi ya zama abun koyi a masana’antar Kannywood

Ali Nuhu

Ga wasu dalilai da muke ganin cewa dan wasan kwaikwayo wanda ake wa lakabi da “sarkin kannywood” yake samun soyuwa a daga mutane da dama

Hakika masana’antar kannywood ta samu babban abun al’fahari kasancewa tare da wannan jarumin a masana’antar.

Ga wasu dalilai 10 da muke ganin cewa sune abubuwan da yasa yan arewa ke farin ciki gannin wannan tauraron wanda aka wa lakabi na “sarkin kannywood” a talabijin;

1. Ya dade yana harkar fina-finai

Tun shekara 1999 Ali nuhu ya fara fitowa cikin fina-finai kuma babban shirin da ya fitar dashi idon jama’a shine “sangaya”.

 

2. Banda Kannywood jarumin jakada ne a masana’antar Nollywood

Wannan jarumin ya nuna mana cewa banda haushen hausa ya kware wajen yin fina-finai cikin harshen turanci.Ya fito a cikin shirin nollywood da dama.

3. Ya amshi lambar yabo da dama

Wannan jarumin ya amshi lambobin yabo bila adadi cikin gida har da ƙasashen waje.

 

4. Shi na kowa ne

Indai ta yadda abokan hamayen shi na masana’antar zasu samu karuwa wannan jarumin yana gaba gaba wajen tabbatar da haka kuma sauran jaruman na alfahari kasancewa tare dashi.

 

5. Yana da ƙwarjini har ƙasashen waje da masana’antu daban daban

Hakika idan muka shiga wasu kasashe zamu ji cewa sunan Ali Nuhu yana yaduwa sanadiyar rawan da yake takawa a wajen yin fim.

6. A harkar fim ya nuna cewa na “Uba da ɗa” ne

Shima dai dan sa Ahmad Ali Nuhu ya fara fitowa a fina-finai hausa tun yana dan yaro bayan ya bayyana ma uban shi cewa shima a gaskiya yana sha’awar yin fim, ganin cewa faduwa ta zo dai dai da zama uban ya mara masa baya amma da sharadi na dole sai ya dage wajen koyan ilimi kuma zai dinga yin haka idan ya samu hutu daga makaranta.

 

7. Da ka ganshi ka gan tambarin Arewa

Shi dai wannan jarumin baya boye ma jama’a a duk inda ya sinci kanshi cewa shi ban dan arewa bane kuma kullum yana neman yadda zai yada al’adar yan arewa ga sauran jama’a.

 

8. Suma masoyan shi suna farin ciki idan suka ci karo dashi

Ganin cewa ya shahara a fannin shirya fina-finai jarumin baya kyamar tarbar masoyan shi a duk inda ya gamu dasu.

 

9. Yana son ƙwallon kafa kuma yana tare da tawagar Nijeriya dari bisa dari

Duk wani wassan kwallo da ya danganci Nijeriya tauraron Kannywood yana gaba gaba wajen goyon bayan tawagar kuma aboki ne ga yan wassan super eagles.

 

10. Ko zamu iya cewa mutu ka raba?

A yanzu dai wannan jarumin yana da shekaru 43 a duniya kuma ya kwashi shekara 19 yana nishatarda mu. Har yanzu jarumin yana nuna cewa kamar yanzu ya fara wannan sana’ar shirya fina-finai kuma ba alamun gazawa tare dashi.

 

Daga nan mu dai muna jinjina ma wannan ƙwararren jarumin da ayyukan da yake yi wajen fadakarwa, nishatarwa tare da ilmantar da mutanen Arewa.

SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94

No comments:

Post a Comment

Post Top Ad

Responsive Ads Here