![Hoton jihar katsina a zanen Nijeriya](https://static.pulse.ng/img/incoming/crop7725728/5826208928-chorizontal-w1600-q90/Nigeria-Katsina-State-map.png)
Matar yar shekara 30 ta shiga hannun hukuma ne bayan wanda tayi ciniki da shi ya kai karar ta ga yan sanda.
Rundunar yan sanda na jihar Katsina ta kama wata mahaifiya wanda ta sayar da yaran ta mata tagwaye a kan N350,000.
Bisa ga rahoto da Gistmania ta fitar ana tuhumar ta da laifuffuka da ya danganci safarar mutane.
Matar yar shekara 30 ta shiga hannun hukuma ne bayan wanda tayi ciniki da shi ya kai karar ta ga yan sanda.
Yayin da take bada amsar tambayar laifin da ta aikata, matar tace ba wai tayi niyar yin haka ba, shaidan ne ya rinjaye ta.
Za'a gurfanar da ita gaban kotu domin yanke mata hukunci.
SOURCE - PULSE.NG posted by Campus94
No comments:
Post a Comment